Hukumar shige da fice ta Ƙasa Immigration ta damka wani dan Najeriya da Kasar Saipros ta fatattake shi daga kasar ta bayan kwanaki uku hukumar tana bashi kula ta lafiya.
Mutumin mai suna Osagie Favour Aigbonghiamon wanda Jirgin Turkish Airline ya sauke shi a filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe dake birnin Ikko a ranar Laraba 28 ga watan Jiya, ya an ci gaba da rike shi a ofishin na Immigration ne bayan da suka lura cewa yana cikin halin bukatar kulawar lafiya.
Mahaifin Mutumin mai suna Mista Lucky Osagie wanda mazaunin birnin Warri ne na Jihar Warri ne na Jihar Delta, ya jinjina wa hukumar Immigration, domin an cewar sa sun shiga halin dimuwa bisa rashin jin duriyar dan nasu.
Ya ce dan nashi ya je Kasar ta Saipros ne don karin ilmi, kuma kagin barin shi Najeriya babu wata alama ta cewa yana da matsalar ƙwaƙwalwa.