Hukumar INEC ta samar da sabbin mazabu 1345 a Jahar Kebbi
Cikin shirye-shiryen zabe mai kamawa 2023, Hukumar zabe ta Jahar Kebbi dama ta Kasa baki daya na kokarin Samar da katin zabe a Jahar.
KARANTA:-Za’a koyawa Mata Yan gudun hijira sama da dubu biyu dinki da hada sabulu a Zamfara
Anyi wannan shirin ne don kusanto da mazabu kusa da masu zabe.
Sannan masu zabe dake tsohuwar mazaba suna da damar komawa sabuwar mazaba don kada kuri’a.
Musa yace sashin wayar da Kai na hukumar zabe zasu cigaba da wayarma mutane Kai dasuje suyi katin zabe a mazaba ta kusa dasu.
Yace tuntuni yaso a fara aikin kasan cewar cutar Covid-19 ta zamo matsala.
Musa yace zamu tabbatar muyi aiki tukuru tare da hadin guiwa da ma’aikata.