Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantun gaba da Sakandare wato JAMB, ta dakatar da Cibiyoyin Rubuta Jarrabawa ta Komfuta, wato ‘CBT Centers’ har goma sha uku daga cikin talatin da biyu dake Jihar Nasarawa saboda rashin bin ƙa’ida.
Magatakardar Hukumar, Farfesa Ishaq Adeleye, ya bayyana hakan a Gidan Gwamnatin Jihar Nasarawa dake Lafiya ranar Alhamis lokacin da yake sa hannu a kan wata Yarjejeniya Fahimtar Juna, wato MoU, da Hukumar Bunƙasa Ci Gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Nasarawa bisa samar da kayan aiki a Cibiyoyin Rubuta Jarrabawar ta Komfuta da Hukumar ta yi a wasu cibiyoyi uku mallakin Gwamnatin Jihar.
Daraktan Yaɗa Labaran shugaban JAMB din, Fabian Okoro, ya ce: abin takaici ne a ce daga cikin Cibiyoyin CBT 32 a Jihar Nasarawa, an dakatar da sha uku daga cikin su. Mista okoro ya ce: “Dakatarwar ta biyo ko dai rashin bin ƙa’ida ko wani abu, ko kuma matsayin bai kai yadda ake zato ba.”
Amma, ya bayyana fatan cewa da sa hannun JAMB a Yarjejeniyar Fahimtar Junan, MoU, da Gwamnatin Jihar, abin zai canza ta fuskar matsayin Cibiyoyin CBT a jihar.
A jawabinsa, Gwamna Abdullahi Sule ya yabi wanda ya gada, Sanata Tanko Al-Makura bisa yadda ya yi gine-gine a cibiyoyin da kuma tallafin JAMB na samar musu da kayan aiki.