By Ishaq Dabai
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sikandire wato JAMB ta sanar da adadin makin shiga manyan makarantun a bana na zangon karatu 2021/2022 a daukacin fadin kasar.
Shugaban hukumar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede shi ya sanar da hakan a yau Talata a Abuja.
Farfesa Oloyede yace hukumar bazata kara amincewa ta dauki dalibai masu maki kasa da 120 na Jarrabawar su ba, sai kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin Ilimi su kuma zasu dauki Dalibin da makin nasu ya soma daga dari (100) zuwa sama, wato dai a matsayin mafi ƙarancin makin shiga kwalejojin Ilimin, da kuma Fasaha.
Ya kara da cewa an cimma wannan matsaya ta mafi ƙarancin makin ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar suka gudanar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tattaunawar an gudanar da ita ne tare da ministan Ilimi Malam Adamu Adamu, wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Ilimin na kasa Arc. Sonny Echono.
Magatakardar hukumar ta JAMB yace taron ya maida hankaline kan yadda tsarin makin zai kasance a zangon karatu na 2021.