A ranar asabar ne 19 ga watan Yuni aka fara rubuta jarabawar shiga manyan makarantu wato JAMB a takaice.
Rahotanni da dama dai sun tabbatar da cewa jarabawar na gudana ba tare da wani tsaiko ba, sai dai hukumar ta sanar da soke wasu cibiyoyin rubuta jarabawar kimanin 25 cikin 800 da ta amince da su.
Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan abin kunya da cibiyoyin suka yi na gaza bin umarni da ka’idojin da aka gindaya musu, tare kuma da fuskantar kalubale da masu jarabawar suka yi.
Wannan na fitowa ne cikin wata sanarwa daga Kakakin Hukumar Dakta Fabian Benjamin inda ta ce cibiyoyin kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito sun hada da Benue State Harry Pass Polytechnic da Makarantar nazarin harkokin jirage ruwa da fasahar zaman dake Delta da Cibiyar Fasahar Sadawar Zamani ta Edo State Oseni Elamah ICT Institute, sai Edo State Givitec CNT centre.
Akwai Edo State Kings Polytechnic da FCT Abuja GEF System limited Public Service Institute of Nigeria dake birnin tarayya Abuja, da cibiyar rubuta jarabawa ta na’ura mai ƙwaƙwalwa ta FOE ICT, da Kaduna State Bethel Baptist High School, da Kwalejin Zabib dake Kaduna.
Kazalika akwai Cibiyar St Albert ita ma dake Kaduna, sai Lagos State Massino Computer CBT da Lagos State IP Soft Technologies limited da makarantar kula da manyan laifuka da gudanar da su dake Legas, da Lagos State Sweet Valley Educational Services sao Lagos state Certified Institution of Shipping da wata cibiyar dake makarantar sakandare ta Al-miyzan ita ma da take legas.
Har wa yau a sanarwar ta Hukumar JAMB, akwai Nasarawa State Aunty Alice Schools da kwalejin Kimiyya da Fasaha dake jihar Ondo sai wata cibiyar dake kwalejin King Emanuel ita dake jihar Ondo gami da Jami’ar Jihar Oshun ta Oduduwa.
Sauran sun hada da kwalejin ilimi na tarayya dake jihar Oyo sai jami’ar Jihar Pilato dake karamar hukumar Bokkos da makarantar St Augustine Academy sai Kaduna State Skolak Resources Limited gami da makarantar sakandaren gwamnati ta Tudun Wada dake birnin tarayya Abuja.
Yanzu haka sanarwar ta umarci wadanda suka rubuta jarabawar Mock da su hanzarta zuwa shafin hukumar don duba sakamakon su.