Hukumar shirya jarabawa Kammala makarantun sakandiren ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar na shekarar 2021 ga daliban jihar Kano.
Jaridar Dimukuradiyya ta ruwaito cewa NECO ta fitar da sakamakon 2021 tun a ranar 29 ga watan Oktoba amma ta hana na gwamnatin jihohin Zamfara, da Adamawa, da Kano, sai Gombe, da Borno da kuma Neja saboda bashin Naira biliyan 1.8 na daliban da suka yi rajista a shekarar 2019.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Aliyu Yusu ya fitar, ta ce hakan ya biyo bayan kokarin da ma’aikatar ilimi ta jihar ta yi na samun kudaden da gwamnatin jihar ta biya domin biyan kudaden jarrabawar NECO da gwamnatin jihar ta yi.
“Fitar da sakamakon a cewar kwamishinan ilimi na jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, zai baiwa daliban damar samun damar shiga jami’o’i da sauran manyan makarantun da suke son shiga,” in ji sanarwar.
“Ya bukaci Daliban da su yi amfani da katinan rajista wajen shiga da kuma buga sakamakon jarabawarsu, ya kuma yi kira ga jama’a da su sanya dabi’ar nuna godiya ga abun da gwamnati ke yi duba da irin kalubalen da ake fuskanta a kan karancin kudaden da ke hannunta. .”
‘’Saboda haka kwamishinan ya yabawa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Murtala Sule Garo da dukkan shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar bisa goyon bayan da suka bayar ta wannan hanyar.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano na cigaba da tallafawa fannin ilimi.