Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta fito da wani shiri na adashin zuwa aikin hajji ga maniyyata, inda za su dinga adana kuɗi kaɗan-kaɗan har su biya kuɗin kujerar.
Wannan ya biyo bayan kasancewar maniyyatan ƙasar nan ba su samu damar sauke farali ba a bana, sakamakon dokokin da ƙasar Saudiyya ta saka na taƙaita aikin hajjin ga waɗanda ke zaune a cikin ƙasar kaɗai, domin kaucewa cunkoson jama’a a dalilin annobar Korona.
Hakan kuma zai baiwa ‘yan ƙasar nan da dama da ba su da halin biyan kuɗin hajjin baki ɗaya, damar su riƙa biya a hankali, taro da sisi, har a cimma biyan buƙata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da biyan kuɗin aikin hajjin ke neman gagarar mai ƙaramin ƙarfi sakamakon ƙaruwar kuɗaɗen guzuri, wanda akasari tashin farashin canji ke haddasawa.
Shugaban hukumar Ahazan Zikirullahi Olakunle Hassan ya ce tun yanzu masu niyyar zuwa aikin hajji a shekara mai zuwa za su iya fara ajiyar kuɗinsu a ƙarƙashin sabon tsarin, har zuwa lokacin da za su shirya gudanar da aikin hajjin ba tare da wata matsala ba.
Hukumar ta ƙaddamar da shirin ajiyar kuɗin ne tare da haɗin gwiwar bankin Ja’iz wanda ya samar da ingantattun hanyoyin sadarwa ta yanar gizo don sauƙaƙa aiwatar da shirin.
https://dimokuradiyya.com.ng/watakila-a-fasa-aikin-hajji-a-bana/
Zikirullah ya ce yarjejeniyar wata sabuwar dabara ce da aka ƙirƙira domin saurin aiwatar da shirin, inda ya ce duk wanda ya yi wannan ajiya ba zai yi asara ba domin ko baya ga amfani da kuɗin wajen yin ibada, haka ma zai amfana da ribar kasuwanci, kana kuma babu iyakancewa ga adadin abinda za’a ajiye ko shekarun da za’a yi ana ajiyar.
Jami’in Kula da adashin gatan Dakta Aliyu Tanko ya ce “mutum na iya yin rijistar dukkan iyalansa sannan kuma ko Naira dubu ɗaya ne ana iya ajiyewa.”
An ƙirƙiro sabon tsarin ne a ƙarƙashin dokar da ta Kafa Hukumar Alhazai ta 2006 a matsayin shirin bayar da gudummuwa ga mabiya addinin musulunci masu son zuwa aikin hajji kuma basu da ƙarfin biyan kuɗin a lokaci ɗaya.
Shugabar Kungiyar Mata Musulmi ta ƙasa Hajiya Halima Jibril da ta wakilci mata a ƙaddamar da shirin, ta ce mata ma ba’a bar su a baya ba a sabon tsarin, akan haka ta yi kira ga al’umma da “su yi cikakken amfani da wannan dama da zasu iya zuwa sauke farali a cikin sauƙi ba tare da wata damuwa ba.”
Hukumar Alhazan ta riga ta ba maniyata damar soma yin rijista a duk faɗin kasar nan.
Babban baƙo a wajen bikin ƙaddamar da shirin shi ne Sakataren Gwamnatin taraiyya wanda Olusegun Adekunle ya wakilta.