Hukumar kare hakkin mai saye da mai sayarwa ta Jihar Kano (KSCPC) ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Inuwa Muhammad Kurmawa mazaunin unguwar Kurmawa dake karamar hukumar birni, wanda yake yin “Sojan Gona” da sunan cewa shi ma’aikacin hukumar ne.
Matashin dai Yana yin amfani da wannan dama yana karbar kudade a wajen mutane musamman ‘yan kasuwa.
A wata sanarwa da Mai magana da yawun Hukumar Musbahu Aminu Yakasai ya aikowa da Jaridar Dimokuradiyya, ya ce Hukumar tana Kira ga al’umma suyi hattara domin irin wadanan bata garin.
Hukumar tace ta Dade tana farautarsa bayan samun rahotannin yadda yake fakewa da hukumar Yana zalintar yan kasuwa anan birnin Kano
Tuni dai hukumar ta mika wanda ake zargin a hannun jami’an ‘yan sanda don ci gaba da bincike.
Comments 1