Wata babbar kotun Majistiri dake zamanta a Kano ta dakatar da manyan motocin safa-safa daga hada-hada a jihar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar da hukumar KAROTA ta shigar akansu.
Dakatarwar dai ta shafi tashar da ke kan titin New road a unguwar Sabon Gari da ma sauran manyan tashoshi.
Hukuncin dai ya biyo bayan yin kunnen uwar shegu da umarnin Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar wato KAROTA na komawa wata sabuwar tashar da ta tanadar musu.
Da take yanke hukuncin, alkaliyar kotun, mai shari’a Rakiya Lami Sani ta ce matakin ya biyo bayan buƙatar hakan da hukumar ta KAROTA ta yi a gabanta.
https://dimokuradiyya.com.ng/masu-babur-mai-ƙafa-uku-a-jihar-kano-sun-koka-game-da-hukumar-karota/
A ƙunshi karar dai, lauyan hukumar ta KAROTA Mutawakkil Ishaq Muhammad ya buƙaci ta dakatar da kamfanoni 15 daga hada-hada a faɗin jihar Kano.
Kotun dai ta umarci kwamishinan ‘yan sanda na jihar da ya rufe tashar motar da ke Sabon Gari da ma sauran tashoshin motocin.
Kamfanonin da ake kara da hukuncin ya shafa sun haɗa da Service Tarzan Motors, Best Way Motors, Landstar Express, Delta Express, Welfare Transport,G.U.O Motors, F.G Onyewe Motors da kuma Godbless Ezenwanta Motors.
Sauran sun haɗa da Young Shall Grow Motors, Ifeanyi Chukwu Motors, Bonnyway Motors, Chimeze Motors, Gobison Motors, S D. Express da kuma First Tarzan Motors.
Mai Shari’a Rakiya Lami Sani ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Satumba.