By Abbas Yakubu Yaura
Ayau ne hukumar kashe gobara ta jihar kano ta ziyarci sansanin masu yiwa kasa hidima na NYSC dan gudanar da gangamin wayar da kan masu yiwa kasa hidimar kan yadda zasu kare kansu daga afkuwar gobara a sansanin dake karamar hukumar Karaye a jihar kano.
Bayan nan hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar kano Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar.
Gangamin wanda Rabiu Abdulkadir na sashen wayar da kai na hukumar ya jagoranta yace makasudin wannan ziyara itace su wayar da su yadda ake kashe gabara da baki da kuma a aikace ta yadda zasu kasheta idan ta tashi.
Abdulkadir yace a lokuta da dama jama’a basu iya amfani da tukunyar kashe gobaraba hakance tasa sukayi wannan yunkuri dan kare rayuwar jama’a da dukiyoyin su.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa masu yiwa kasa hidimar sun nuna jindadin su da kuma murna dan gane da wannan ziyara suna fatan zasuyi aiki tare dasu.