Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kano, ta ce titin Kano zuwa Zaria zuwa Kaduna ya kasance wurin da hukumar ke fuskantar kalubale yayin da masu ababen hawa ke tukin ganganci a kan hanyar da a halin yanzu ake gyarawa.
Kwamandan hukumar FRSC, Zubairu Mato ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Mato ya koka da cewa masu ababen hawa da ke bin hanyar su kan yi amfani da aikin gyaran hanyar wanda tuni aka kammala wani bangare domin wuce gona da iri, kuma a mafi yawan lokuta yakan haifar da taho mu gama.
Kwamandan sashin ya ce, ya tura jami’an sa da kayan aikin su zuwa bakin hanya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a kan hanyar.
A cewarsa, “A halin yanzu, titin daya tilo da ke fuskantar kalubale da muke fama da ita ita ce hanyar Kano zuwa Zariya zuwa Kaduna. Kuma muna kan halin da ake ciki.
Kwamandan sashin ya ci gaba da cewa rundunar ta samu nasarar tantance hadurran da ba a taba samu ba a kan hanyar Kano zuwa Bauchi da Kano zuwa Azare da dai sauransu.
Comments 1