Daga: Ibrahim Hassan Hausawa
Hukumar da ke kula da harkokin ‘yan sanda (PSC) ta yi wa tsohon shugaban riko na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Ta’annati (EFCC) karin girma Ibrahim Magu.
Ikechukwu Ani, mai magana da yawun PSC, ya sanar da daukaka matsayin Magu zuwa matakin Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (AIG) a ranar Litinin.
Ya ce an yi wa Magu karin girma ne tare da wasu manyan jami’ai a babban taron hukumar karo na 15 a ranar Juma’a.
Ya kara da cewa an nada mukaddashin DIG John Ogbonnaya Amadi a matsayin babban mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda, yayin da Zama Bala Senchi kuma aka nada shi a matsayin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda.
Ya ce baya ga Magu, kwamishinonin ‘yan sanda bakwai sun samu karin girma zuwa mataimakan sufeto-janar na ‘yan sanda.
Hukumar ta kuma amince da karawa mataimakan kwamishinoni 23 karin girma zuwa mukamin kwamishinonin ‘yan sanda na gaba; Mataimakan kwamishinoni 31 ga mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda da manyan Sufeto Janar na ‘yan sanda 63 sun samu karin girma zuwa mataimakan kwamishinonin ‘yan sanda.