Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC), karkashin jagorancin shugabanta, tsohon IGP Musiliu Smith, bayan kammala taronta karo na 13 a Abuja wanda ya gudana a ranakun Litinin 20 ga watan Disamba da Talata 21 ga watan Disamba, ta umurci kwamishinan ‘yan sanda, CP Abdulkarim Dauda da ya mika takardarsa ta ritaya tare da nan take don keta tsarin tsawaita wa’adin aiki ba bisa ka’ida ba.
CP Abdulkarim Dauda wanda ya kasance Babban Jami’in tsaro (CSO) ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuma zai yi ritaya daga hukumar NPF bayan ya cika shekaru 35 yana aiki, an kuma umurce shi da ya mayar da albashin da ya karba daga hannun ‘yan sanda daga watan Janairun 2020 zuwa yau.
Kwamishinan yada labarai na hukumar PSC, Mista Austin Briamoh wanda ya bayyana haka a wani taro bayan zaman majalisar ya ce CP Dauda ya yi ikirarin cewa an kara masa aiki ne a lokacin tsohon IGP Mohammed Adamu zuwa shekara ta 2021.
Amma Mista Briamoh ya bayyana cewa yayin zaman majalisar, an binciki dukkan bayanan kuma babu inda ko wata takarda da ta nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin wa’adinsa yayin da kuma babu wani tarihin da ya nuna lokacin ko kuma inda IGP Adamu ya ba shi izinin kara wa’adin aikinsa.
Bugu da kari, Mista Braimoh ya bayyana cewa an bankado haka ne lokacin da tsohon CSO ya aike da wasika zuwa ga PSC inda ya bukaci a kara masa girma zuwa matsayi na gaba na mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda yana mai cewa ya cancanci hakan bisa ga karin wa’adin don har yanzu yana cikin karfi.
“Don haka hukumar PSC ta gano wasu kura-kurai a kan batun kara wa CP Abdulkarim Dauda ba tare da bin ka’ida ba, sun yi watsi da karin wa’adin tare da mayar da ritayarsa zuwa ranar 1 ga watan Janairun 2020 a lokacin da ya kamata ya yi ritaya,” in ji Mista Braimoh.
” Ba mu da wani tarihi da ke nuna cewa Shugaban kasa ya kara wa’adinsa. Don haka, mun nemi ya tafi. Zai yi ritaya ya mayar da albashin da ya karba daga Janairu 2020 har zuwa yau. Mun ma yi adalci da jin kai domin lokacin da zai yi ritaya an kara masa tsawo.
“Wannan cin zarafi ne da dokar ‘yan sanda. A kan haka ya roki a kara masa girma shi da yake kan wa’adi ba bisa ka’ida ba”.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa hukumar ta dauki tsawon lokaci wajen aiwatar da karin wa’adin ba bisa ka’ida ba a lokacin da jami’in ya ke karbar albashi da kuma kula da wasu, Braimoh ya ce, “hukumar PSC ce tana da tsarin mulki. Muna bin tsarin da ya dace kuma muna tabbatar da cewa an yi amfani da doka cikin adalci da biyayya. Kamar yadda kuke gani, har ma mun yi adalci da Rahama.
Ya jaddada cewa ritayar CP Dauda tana nan take.