Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) a ranar Juma’a ta bayyana cin zarafin da aka kai wa Insfecta Teju Moses, ‘yar sandan da ke tare da Farfesa Zainab Abiola, a matsayin dabbanci da rashin mutunci. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Mista Ikechukwu Ani, shugaban sashin kula da kafafen yada labarai da hulda da jama’a na PSC, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce harin da aka kai Teju barazana ce ga tsaron kasa kai tsaye idan aka yi la’akari da yunkurin yin izgili ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da abin da hakan ya ke nufi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jihar Kano Na Buƙatar Ruwan Sha Lita Miliyan 200 A Kullum – Inji Kwamishinan Ruwa
Ani ya yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da hannu a wannan abin kunya, sannan ya bukaci hukumar ‘yan sanda da ta sake duba ayyukan Sashen Kariya na Musamman (SPU).
Kakakin na PSC ya ce sun yi wannan kiran ne domin a tabbatar da cewa ‘yan Najeriya kalilan ne da suka cancanci irin wannan kariya kawai ake yiwa wannan hidima.
Ya ce, “Hukumar ta fusata kan yadda ‘yan Najeriya ke cin zarafin dokokin ‘yan sanda da a yanzu suke amfani da su a matsayin alamomin matsayi ko mayar da su gida suna taimaka wa masu tsaftace muhallansu dafa abinci ko yin ayyuka marasa tushe.
“Tare da matsalolin tsaro da ke addabar al’ummar kasar nan akwai bukatar a sako jami’an ‘yan sanda da dama da ke yawo a gidaje mutane masu zaman kansu da bin manyan mutane.”
Ani ya kuma bukaci manyan jami’an ‘yan sanda da su gaggauta dakatar da wannan al’ada tare da mayar da hankali wajen aikin ‘yan sanda da kare marasa galihu a Najeriya.
Idan za a iya tunawa cewa Rebecca da wani mutum da ake zargi sun yi wa Teju wulakanci.
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, ta tabbatar da cewa an tsare Farfesa Zainab Duke Abiola, da ma’aikatan gidanta, ciki har da ‘yar aikin gidan Rebecca Enechido, wacce ta ci zarafin wata jami’ar Teju Moses, a gidan yari na Suleja.
A WANI LABARIN KUMA; Kaduna: Yan Bindiga Sun Sace Wasu Jiga Jigai A Jam’iyyar APC
An yi garkuwa da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna a wani hari da aka kai a hanyar Kaduna zuwa Kachia a jihar Kaduna.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa harin ya faru ne a wani wuri mai suna Tashar Icce, wanda ke da tazarar wasu mitoci daga al’ummar Kujama da ke yankin Kajuru a jihar