Hukumar hana fasa qwauri ta kasa reshen Kano da Jigawa ta bayyana shiryawar ta domin aiki da kungiyar yan jaridu ta Jihar Kano, don tafiya tare a ayyukan da take.
Kwanturolan Hukumar Muhammad Umar ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi Bakuncin shugabanninnm kungiyar a ofis dinsa.
Muhammad Umar ya bayyana yan jarida a matsayin wani kashin baya wajen samar da ci gaban al’umma, wanda kuma suke da tasiri wajen sanar da mutane abun da ke faruwa, kuma hadakar domin tafiya tare zata taimakawa hukumar Kwastom din kan irin aikace aikacen da take yi.
Anasa jawabi mataimakin Kwanturolan Hukumar M.A Hassan ya ce hukumar a koda yaushe na tabbatar da cewa jami’an ta maza da mata na aiki yadda doka ta tanadar musu.
Baya ga haka, ya bayar da tabbacin cewa duk wanda aka samu cikin jami’an su da laifin taka doka, to kuwa Doka shima zata taka shi daidai yadda ya debo.
Da yake jawabi tunda fari, sakataren kungiyar ta Chapel Comrade Musbahu Aminu Yakasai, yace sun je hukumar ne domin jaddada alakar aiki a tsakanin su da hukumar.
Ya kuma kara da cewa a shirye suke domin ci gaba da sanar da al’umma irin aikace aikacen hukumar, da nufin al’umma su ci gaba da basu hadin kai.