By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Kwastam ta Najeriya dake Kaduna a ranar Juma’a ta ce ta kama wata mota makare da naman jakuna da buhu 12 na tabar wiwi na sama da Naira miliyan 250 a cikin wata guda.
Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna, Kwanturolan Ayyuka na Tarayya na shiyyar “B” dake Kaduna, Albashir Hamisu, ya bayyana cewa an boye kayan ne da dabara a cikin buhu 2,348 da fakiti 126 da kudin harajin ya kai Naira miliyan 251,701.
Hamisu ya bayyana cewa ma’aikatan sun sami makamancin haka guda 144 tsakanin 24 ga watan Fabrairu zuwa 23 ga watan Maris, 2022.
Ya lissafo sauran kayayyakin da aka kama a cikin wannan lokaci da suka hada da buhunan tramadol 3,700 da buhuna 460 na fakitin D6.
A cewarsa, an kama wani haramtaccen magani mai suna D5, wanda masana suka ce yana yin aikin sa iri daya ne da tramadol, an kuma mika shi ga jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa.
Sannan ya ce an kama su ne ba tare da jami’an NDLEA ba, kuma saboda hadin gwiwar hukumomin ne aka mika wa hukumar kayayyakin.
“Sauran kayayyakin da aka kama sun hada da buhunan shinkafar kasar waje buhu 1,100, mai nauyin kilogiram 50kg, motocin da aka yi amfani da su guda bakwai, bale 128 na kayan sawa na kasashen waje; Motoci 11 a matsayin hanyar isar da kayayyakin fasa-kwauri, da kayan masaku guda 100.
Jami’in ya kara da cewa, hukumar ta kuma kama buhu 13 na sabbin takalmi na kasashen waje, katan 514 na spaghetti na kasar waje, katan 18 na madara da kuma katan 11 na biskit din da wa’adin sa ya kare daga kasashen waje.
Kwanturolan ya kuma lissafta makudan man kayan abinci jarka 65 na kasashen waje, da buhu 319 na PMS, da buhu 336 na snuff (Taba) da dai sauransu.
Ya ce an kama wani da ake zargi da laifin safarar naman jakuna ta barauniyar hanya, kuma tuni aka mika shi ga rundunar ‘yan sanda a Kaduna domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.
Hamisu, ya ce hukumar ta NCS za ta ci gaba da yin iyakacin kokarinta wajen tsaftace Najeriya, tare da tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta gindaya domin ci gaban al’ummarta.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya masu kishin kasa da su amince da hadin gwiwa da Hukumar NCS ta hanyar ba da ingantattun bayanai don taimakawa wajen magance ayyukan fasa-kwauri a yankin.
A baya-bayan nan dai jaridar Dimokuradiyya ta bayar da rahoton yadda wasu marasa kishin kasa ke safarar naman jakuna a wasu lokutan zuwa cikin kasar, lamarin da hukumomin kiwon lafiya suka sha bayyanawa a matsayin haramtacce kuma ba a iya amfani da su saboda illar da ke tattare da hakan.
Biyo bayan kama irin wannan da aka yi a jihar Edo, jaridar PUNCH ta ruwaito mataimakin daraktan sashen kula da lafiyar dabbobi da kiwon lafiya na ma’aikatar noma da albarkatun kasa, Dakta Peter Osagie, yana cewa “cin naman jaki baya cikin naman da aka sanyawa doka ga dan Adam a jihar Edo; su (masu fasa kwauri) suna yin wannan sana’a ne a cikin duhu da rufa-rufa.
“Wasu daga cikin wadannan dabbobin da ake sarrafa su don amfanin mutane ba a yi musu wani nau’in bincike ba. Duk wata dabbar da ba a bincika ba kafin a gabatar da ita don cin mutumci, ana ganin ba ta da lafiya,” in ji Osagie.
Don haka an shawarci jama’a da su yi hattara da irin naman da suke ci; su zama masu bin doka da oda, yayin da ka daina duk wani nau’i na safarar miyagun ƙwayoyi.
(NAN)