Hukumar Kwastam ta kasa reshen jihohin Kano da Jigawa, ta kama sama da Buhunhunan guda 3,387 na shinkafar kasar waje, da gwanjo, da taliya Yar kasar waje, da kwaya da sauran haramtattun kayayyaki da darajarsu ta haura N1.2bn.
Kwanturolan hukumar kwastam mai kula da shiryar Kano da Jigawa, MA Umar, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano ranar Talata, ya kuma ce an kama kayayyakin ne tsakanin watan Maris zuwa Afrilun shekarar 2022 a jihohin biyu.
Kwanturolan ya ce, a tsawon wannan lokaci, rundunar ta samu karin kudaden shiga zuwa sama da Naira billiyan 14, daga Naira mbilliyan 9.6 da take samu a baya.
Ya ci gaba da cewa, “A kokarinmu na yaki da ayyukan fasa kwauri, rundunar mu ta samu gagarumar nasara ta kwace buhunan shinkafa ‘yan kasashen waje guda 1,593 da kudinsu ya haura Naira Milliyan 46.7, kunshi 275 na tabar wiwi da kuma kwalayen tramadol bakwai.
“Sauran kayayyakin da aka kama a cikin wannan lokaci sun hada da katan 1,237 na sabulun kasar waje wanda kudinsu ya kai Naira Milliyan 16.1, katan-katan din Taliyar kasar waje guda 151, kunshi 131 na tufafin gwanjo, sai kunshi kwayoyin maye guda 34,940.
Kwanturolan ya kara da cewa, “Jimillar adadin kayayyakin da aka kama ya kai na naira 1,966,115,027.15.
Ya ci gaba da cewa, za a mika magungunan da aka kama ga hukumar yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin ci gaba da gudanar da bincike.
Kwanturolan ya kuma gargadi mutane da su daina yin fasa-kwauri saboda abin da ya bayyana a matsayin illa ga tattalin arzikin kasar nan, yana mai cewa wadanda suka gaza za su gamu da fishing Hukuma.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ruwaito cewa, rundunar ta kuma ba wa wasu fitattun ma’aikatan da ke aiki a jihohin biyu kyauta, musamman wadanda ke aiki da sashin biyan albashi.