By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar hukumar kwastam ta Najeriya dake yankin Seme ta kama hodar ibilis mai nauyin kilogiram 11.913, wanda ake kyautata zaton kudin ta ya kai naira 3,916,624,147.00.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam ta Seme DSC Hussaini Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Ya ce rundunar a ranar Larabar da ta gabata ta kama jarkokin man fetur guda 1,065 tare da biyan harajin naira 10,041,198.00.
“Hakan ya biyo bayan rundunar yankin ta fara sintiri a kan fasa kwaurin man fetur a rafi da ke cikin Seme da Badagry,” inji shi.
“Kwanturolan hukumar ta Kwastam, Bello Mohammed Jibo ya jaddada cewa farmakin ya dakile ayyukan masu safarar man fetur da kuma manufar kama su a duk inda suke. Ya kuma ba da tabbacin cewa rundunar za ta ci gaba da sanya rayuwa cikin rashin kwanciyar hankali ga marasa kishin Najeriya da ke sana’ar sayar da haramtattun kayayyaki a yankin.
“Da yake magana tun farko kan kama hodar Iblis, Jibo ya bayyana cewa an kama abun ne a kan titin Seme- Badagry da misalin karfe 09:00 na safiyar ranar Lahadi 23 ga watan Janairu, 2022.
“Saboda haka, hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa ta yi gwajinta tare da tantance ta, kuma an same ta da hodar iblis mai nauyin kilogiram 11.913.
“Yayin da ta yaba da hadin gwiwar hukumomin ‘yan uwa da masu ruwa da tsaki a kan iyakar Seme, CAC ya nanata kudurin jami’an sa da maza wajen aiwatar da manufofin kasafin kudi na gwamnati don ci gaban kasa baki daya.”
Comments 1