Hukumar Kwastan ta Nijeriya, NCS a ranar Laraba ta karawa jami’anta 28 mukami dake aiki a yankin Seme.
Da yake yiwa jami’an da suka samu Karin mukami a iyakar Seme dake jihar Legas, mukaddashin Kwanturola na hukumar dake yankin, Chedi Wada, ya ce Karin wannan mukamin da aka yi musu kamar Karin wadansu ayyukan ne a kawukansu.
Kuma ya tabbatar musu cewa dukkanin wani jami’i da aka yi masa Karin mukami, wannan mukamin na zuwa da Karin sabon aiki ne, a don haka ya shawarce su da su zamo masu jajircewa da sadaukarwa.