Kwanturolan hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS), Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya amince da nadawa tare da sauya matsayin wasu ma’aikatan hukumar guda 20 na aiki.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Kwanturola Timi Bomodi ya fitar ranar Alhamis a Abuja, ta tabbatar da karin matsayin da nadin.
Sanarwar ta ce amincewar ta biyo bayan ritayar da wasu ma’aikatan hukumar suka yi bisa doka.
KU KARANTA KUMA Hukumar Kwastom Ta Kama Kayan Sojoji Da Yan Sanda Kwanaki Kafin Zaben 2023
Ya kuma kara da cewa atisayen shi ne don inganta dabarun bayar da ayyuka da inganci.
Sanarwar ta ce, babban kwanturolan, yayin da yake mika godiyarsa ga ‘yan hukumar da suka yi ritaya bisa gagaruwar aikinsu, ya taya sabbin jami’an da aka nada murna.
Ta ce Ali ya bukaci sabbin jami’an da aka nada da su yi aiki tukuru wajen ganin hukumar ta samu nasarori masu yawa a ayyukanta na samar da kudaden shiga, dakile fasa kwauri da kuma saukaka harkokin kasuwanci.
Sake nadin ya nuna cewa an zabo sabbin ma’aikatan ne daga sassa kamar Tariff and Trade, Enforcement Inspection & Investigation, da dai sauransu.
A Wani Labarin Kuma NAHCON Ta Gana Da GACA, Ta Bada Tabbacin Gudanar Da Aikin Hajji Ba Tare Da Matsala Ba
Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa Alhazan Najeriya tabbacin gudanar da aikin hajjin 2023 ba Tare da Wata matsala ba.
Hukumar ta yi wannan alkawarin ne a lokacin da ta kai ziyara babban ofishin hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta GACA a Jeddah ranar Alhamis.