Hukumar hana fasa qwauri ta kasa reshen Sokoto da Zamfara ta tabbatar da yunkurin neman hadin kai a tsakaninta da takwarorinta wajen karfafa tsaro a iyakokin jihohin da kuma jamhuriyar Nijar.
Sabon Kwanturolan hukumar Musa Omale ne ya tabbatar da hakan yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai kan iyakokin, yana mai cewa ta hanyar karfafa tsaron iyakokin za a samu ci gaba mai dorewa a tsakanin Najeriya da Nijar. Kamar yadda gidan talabijin na TVC ya rawaito.
KU KARANTA: Dattawan Arewa Sun Musanta Zaɓar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Su
Musa Omale ya kuma gana da masu rike da sarautun gargajiya a wadannan yankuna, da sauran alumma tare da bukatar su bashi hadin kan da ya kamata domin cimma burin da suka sanya a gaba.
A wani labarin kuma hukumar ta Kwastom reshen jihar Kebbi umarni tayi da kakkausar murya ga wadanda ke safarar man fetur din kasar nan zuwa wasu kasashen dake makwabtaka da Najeriya, yana mai cewa wannan babban laifi ne da idan suka kama mutum zasu yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.
Sabon kwanturola na hukumar a jihar Kebbi, Konturola Ben Oramalugo a lokacin da yake zantawa da manema labarai ya ce rundunar ta samu nasarar kama wasu kayayyaki guda 14 da suka hada da lita 8,975 ta man fetur da aka loda a cikin kwalayen lita 25 da sauran kayayyaki da kudinsu ya kai Naira 91,518,924.
A wani labarin kuma: Uba Sani Ya Kai Ziyarar Bangirma Ga Sarkin Zazzau
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a ƙarƙashin Jam’iyar APC Sanata Uba Sani ya kai ziyara ga Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu a fadar sa dake garin Zaria.
Ɗan Takarar ya kai ziyarar ne a matsayin wani kokarin sa na ziyarar bangirma da kuma kai ziyara don neman goyon baya.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook, wanda gidan Jarida na Dimokuraɗiyyar ya samu.