Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Ghebreyesus, ya ce hukumar na hada kai da ƙasar Guinea inda aka samu bullar cutar zazzabin Ebola.
Ya ce tallafin da za a yi wa kasar zai hada da riga-kafin Ebola da kula da masu cutar sannan WHO za ta yi aiki da gwamnatocin kasashe makwabta.
Liberia da Saliyo na daga cikin kasashen da aka ayyana suna cikin hadari saboda kusancin wajen da annobar ta bulla da su.
Amma WHO ta ce a yanzu ta shirya tsaf don yaki da annobar a kan shekarar 2013 lokacin da sama da mutum dubu 11 suka mutu sakamakon annobar a sassan yammacin Afirka.