Hukumar leken asirin Somaliya ta yi gargadi game da wani shiri da ake zargin mayakan al-Shabab da ke kawance da al-Qaeda na iya kai wa shugaban kasar da firaminista hari.
Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Kasar (Nisa) ta bayyana hakan ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter cewa ta sanar da shugabannin kasar game da shirin Kai harin na Al-shabab.
Sai dai Hukumar ba ta yi Wani cikakken bayani ba dangane da lamarin, amma ta ce tana bin diddigin duk wanda ke da hannu a yunkurin kai harin.
Idan ba’a manta ba, A baya-bayan nan ne kungiyar ta kai hari a wani katafaren filin tashi da saukar jiragen sama da ke dauke da ofisoshin jami’an Majalisar Dinkin Duniya, da ofisoshin jakadancin kasashen waje da kuma ofisoshin diflomasiyya daban-daban a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.
Har ila yau, ta kai harin kunar bakin wake guda biyu a tsakiyar garin Beledweyne, inda aka kashe akalla mutane 48 ciki har da wata mace ‘yar majalisar dokokin tarayyar Somaliya.
Comments 1