A cigaba da fafatawa a gasar Premier ta kasar nan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars zata kece raini da takwararta ta Wiki Tourists.
Za ayi wasanne a ranar Lahadi 12 ga watan da muke ciki da karfe hudu na yamma, a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar mata.
Kano Pillars ce zata karbi bakubcin wasan, to sai dai za ayi wasanne ba tare da ‘yan kallo ba.
Hakan na daga cikin sharadin da hukumar dake shirya gasar league ta kasa (LMC) ta bada umarni.
A baya dai hukumar ta maida Kano Pillars cigaba da fafata wasanta na cikin gida a filin wasa na MKO Abiola dake Abuja bayan da magoya bayan kungiyar suka farmaki ‘yan wasan Katsina United.
Yanzu haka dai kungiyar ce ta nemi a sauya mata wajen buga wasan, kuma hakan ce ta faru, domin kuwa an sassauta musu hukuncin na cigaba da yin wasa a gida amma batare da ‘yan kallo ba.