Gwamnatin jihar Kano ta karbi gudunmawar sabbin motocin daukar marasa lafiya na zamani guda 4 daga hukumar da ke yaki da cutar kanjamau ta kasa (NACA) wadda ke samun tallafi daga asusun Global Fund da nufin karfafa daukar matakai da ayyukan kiwon lafiya.
A lokacin da yake karbar motocin daukar marasa lafiya a gidan gwamnatin Kano, Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya yabawa hukumar ta NACA da Global Fund bisa wannan tallafin da ya ce zai karawa kokarin gwamnati na samar da dauki cikin gaggawa domin karfafa harkar lafiya a fadin jihar.
“Ina so in yaba wa kokarin masu hannu da shuni kan goyon bayan da suke baiwa Gwamnatin Jiha ta hanyar da suke yi na inganta ayyukan jinya na gaggawa da kiwon lafiya inji shi”.
Tun da farko babban daraktan hukumar ta NACA Dr.Gambo Aliyu Gumel wanda Daraktan ayyuka na musamman Baidi Gajo Muhammed ya wakilta ya bayyana cewa sun bayar da tallafin ne domin yabawa kokarin gwamnatin jihar Kano na yaki da cutar kanjamau da sauran ayyukan kiwon lafiya.
“An ja hankalinmu da jajircewar da gwamnatin jihar Kano ta yi na samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga al’ummarta, in ji shi”.
A nasa jawabin, kwamishinan lafiya na jihar Dr.Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce motocin daukar marasa lafiya na dauke da kayan aikin jinya da na’urori, ya kuma bada tabbacin za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.