Hukumar jindadin Alhazai ta jihar kano ta zargi Kamfanin jirgin da aka baiwa aikin jigilar Alhazan Kano, da jan kafa wajen haifar da tsaiko yayin jigilar maniyyatan.
Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Kano Muhammad Abba Danbatta shine yayi wannan Koke yayin hira da manema labarai da ya gudanar yau a Ofishin sa.
Ganawar tasa na zuwa ne bayan da hukumomin kasar Saudiyya, suka sanar da rufe shigar jiragen da bana na kasar ba, da nufin kai Maniyyatan, tun a daren jiya Lahadi.
A cewar Danbatta yanzu haka akwai sauran Maniyyatan Kano dake dakon kai su kasar Saudiyya, kuma zasu yi amfani da jirgin Flynas wajen ganin an kaisu kasa mai tsarkin.
Kazalika ya yabawa gwamnatin Kano bisa jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje inda yace gwamnan dakansa ya ziyarci Hukumar jindadin Alhazai ta Kasa duk domin samarwa alhazan Kano Mafita.
Yace Alhazai da dama ne Jirgin ya jibge tsawon awanni 24, kuma har yanzu basu yi wani cikakken bayani dan gane da wannan tsaikon da maniyyatan suka fuskanta ba.