By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar hana fataucin bil’adama ta kasa (NAPTIP) tace ta samu sama da mutane 70 wadanda suke safarar mutane a jihar Abia cikin watanni shida.
Shugaban gudanarwa na Hukumar NAPTIP a jihar Abia, Misis Nkemdirim Okafor, ta bayyana hakan a wata tattaunawa data yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a Umuahia.
Tace an samu kararraki 70 tsakanin watan Yuni zuwa Disamba na wannan shekara da hukumar ta fara gudanar da ayyukanta a jihar.
A cewar Okafor, akwai mutane 27 da ake tuhumarsu akan lamarin, sannan kuma mutane shida da ake tuhuma suna jiran shari’a.
Tace wadanda abin ya shafa galibi ‘yan mata ne da kuma mata da aka yi lalata dasu.
Kazalika akwai batun sayar da jarirai, lalata da mata, cin zarafin mata da daukar yara ba bisa ka’ida ba, in ji ta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Okafor tace an garzaya da wadanda ake zargin zuwa ofishin hukumar dake Enugu domin gurfanar da su a gaban kuliya tun da ofishin Abia ba shi da wurin tsare masu laifi a halin yanzu.