Darakta Janar na Hukumar Hana saffarar Mutane ta Kasa NAPTIP, Sanata Basheer Garba Muhammed ya ce, jimillar mutane 104 hukumar ta ceto daga hannun masu saffarar mutane, lokacin da suke kokarin haurar da su zuwa kasashen Turai ta Libya.
Ya bayyana hakan ne a a jiya Talata a garin Abuja, ya yin da ya ke jawabi kan sabon harin da Hukumar ke kaiwa masu fataucin mutane a fadin kasar.
A cewar Shugaban hukumar, an kuma kama mutane takwas, a yayin da ake kokarin kama sauran membobin kungiyar masu fataucin mutanen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NiMet ta yi hasashen ambaliyar ruwa a jihohi 34 dake Nigeria
“Duk inda masu fataucin suka je don yaudara da ɗaukar waɗanda abin ya shafa, koyaushe za su sadu da mu a wurin fita.” Inji shi.
“Mun kudiri aniyar hanasu wannan harkar kasuwancin, har sai idan sun daina munanan ayyukan da suke yi, kuma suka sami wani halattacciyar sana’ar da za su yi,”
Kazalika Shugaban hukumar na NAPTIP ya yaba wa sauran hukumomin tsaro saboda hadin gwiwar su da NAPTIP, wanda ya yi sanadiyyar cafke wadanda ake zargi tare da ceto wadanda abin ya shafa.