Hukumar dake kula da kafafen watsa labarai ta kasa NBC ta bada umarni wa kafafen watsa labarai da suka hada da Rediyo da talabijin da su gaggauta rufe shafukansu na tuwita.
Wannan umarni na zuwa ne yan kwanaki bayan da gwamnatin tarayya ta bada umarnin haramcin amfani da kafar tuwita a ƙasarnan.
Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar Armstrong Idachaba a sanyin safiyar yau Litinin, ya ce dole ne kafafen radiyo da talabijin sun datse duk wata alaka dake tsakaninsu da tuwita.
Da ma dai tun a ranar Juma’a ne gwamnatin tarayya ta haramta amfani da shafin na tuwita, a wani mataki na hana bazuwar labaran karya a kasar.