By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Kididdiga ta Najeriya, NBS, ta karawa Mista Joel Ichedi zuwa mukamin Darakta, tare da wasu mutane takwas, kamar yadda wata takardar da hukumar ta fitar a makon jiya.
Sauran wadanda aka karawa mukamin darakta sun hada da, Mista Adebisi A.T. da Ameh G.E., sai Anyakora A.C., tare da Babalola D.A., Maigida I.Z., da Mustapa A. D., Oriokpa V.I. da kuma Adegbe A.
Kazalika Ichedi ya kasance shine mai kula da sashen sadarwa da hulda da jama’a na hukumar ta NBS.
An dai haifi Ichedi a Odugbo dake karamar hukumar Apa ta Benue,sannan Ichedi ya kammala karatun sa a fannin tattalin arziki a jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1988.
Bayan kammala karatunsa na digiri na jami’a, Ichedi ya shiga aikin ofishin kididdiga na gwamnatin tarayya a lokacin a shekarar 1992 a matsayin masanin kididdiga-2.
Sannan Ichedi ya kuma samu shaidar kammala karatun digiri a fannin kididdiga, Talla da hulda da jama’a, aikin jarida da MBA daga Jami’ar Ibadan, Cibiyar Nazarin aikin Jarida ta Najeriya da Jami’ar Fasaha ta Jihar Enugu, bi da bi. Har ila yau, yana da takardar shaidar difloma a Cibiyar Hulda da Jama’a ta Nijeriya, NIPR.
A yanzu haka dalibin da ya kammala karatunsa na digiri na biyu a fannin tattalin arziki a Jami’ar Jihar Nasarawa inda yake gudanar da bincike mai zurfi a kan illar rikicin manoma da makiyaya ga rayuwar al’ummar Karamar Hukumar Agatu. Yana da aure da ‘ya’ya.