Hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) ta tabbatar da bullo da fadada ilimin koyan aikin jarida zuwa sassa 3 daban-daban da kuma shirin aiwatar da irin wannan a cikin karatun kimiyyar kwamfiyuta.
Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Idris Mohammed Bugaje ne ya bayyana hakan a Kaduna a wajen rufe taron kwana biyar na sabbin manhajojin da manyan masu ruwa da tsaki suka yi a ranar Juma’a.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Babban Sakataren NBTE wanda mataimakinsa na musamman Malam Ibrahim Bashir Bello ya wakilta, ya ce sabbin kwasa-kwasan da aka fara gabatar da su sun hada da aikin jarida da na karatuttukan sadarwa da dabarun sadarwa da na yada labarai sannan sai kuma harkar fina-finai da multimedia.
KARANTA HAKANAN NBTE Ta Tabbatar Da Gano Haramtattun Makarantun Fasaha A Najeriya
Farfesa Idris Bugaje ya ci gaba da cewa, za a yi tunanin kwasa-kwasan ne a matakin Higher Diploma a dukkanin cibiyoyin koyar da fasaha da sana’o’i da kwalejojin ilimi a fadin kasar nan, ya kuma bukaci cibiyoyi daban-daban da su dauki nauyin karatun malaman domin su sabunta iliminsu kan kwasa-kwasan.
Babban Malami a sashen kpyar da aikin jarida, Abdu Gusau na kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya a jijar Zamfara, Mallam Lawal Umar Maradun ya yabawa Hukumar NBTE bisa wannan ci gaban da ta samu inda ya ce ta kawo wa Malaman kwalejojin sauki da a yanzu za su iya maida hankali kan wani fanni na musamman.
Wani ma’aikaci mai suna Mista Jide Johnson ya jaddada cewa sabbin manhajojin sun samu karbuwa daga kwararrun da ake girmamawa kuma za su ba ‘yan jaridun Najeriya kayan aikin jarida na zamani da sauran su.
A Wani Labarin Kuma Wannan Dimokuradiyya Muke Ba Mulkin Soja Ba – Garo Ya Caccaki FG
Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Murtala Sule Garo ya caccaki wa’adin da gwamnatin tarayya ta bayar domin cire tsofaffin takardun kudin naira.
Tsohon kwamishinan kananan hukumomin ya koka kan lamarin a lokacin da yake jawabi a taron yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Dambatta.