Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kaftin Musa Nuhu a matsayi sabon Daraktan hukumar lura da sufurin jiragen sama ta Nijeriya da aka fi sani da NCAA a takaice.
Kaftin Nuhu ya canji Kaftin Muthar Usman ne wanda ya kasance Daraktan hukumar kafin Kaftin Nuhu. Wannan sanarwar ta fito ne daga Daraktan hulda da jama’a a hukumar jiragen sama, James Odaudu, wanda ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Kafin nadin da aka yiwa Nuhu, shi ne wakilin Nijeriya a kungiyar lura da jiragen sama na duniya wato ICAO.
Yana da digiri na biyu a bangaren kasuwanci jiragen sama, kuma ya kasance wanda yake jagorantar jiragen saman fadar shugaban kasa, kuma ya kasance har wala yau babban jami’in lura da jiragen sama.
Sannan har wala yau ya yi aiki a wurare da daman gaske a bangaren jiragen saman. Sannan shugaban kasa Buhari ya amince da nadinMahmoud Ben-Tukur a matsayin sabon wakilin Nijeriya a kungiyar ICAO.