By Abbas Yakubu Yaura
Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya ta bukaci shugabannin makarantu da kar su bari masu zafin jiki sama ma’aunin 38°C shiga cikin wuraren makaranta.
Wannan shi ne kamar yadda cibiyar ta ba da shawarar yin amfani da na’urorin gwajin gaggawa da aka amince da su a makarantu don gwada ɗalibai da membobin ma’aikata bayan an dawo da ga hutu.
NCDC ta ba da wannan shawarar a cikin sabon rahoton halin da ake ciki na cutar COVID-19 da aka gabatar wa manema labarai a Abuja.
A cewar cibiyar, gano bambance-bambancen Omicron wanda aka gano yana iya yaduwa ya jaddada bukatar tabbatar da aiwatarwa da kuma bin matakan kiwon lafiyar jama’a game da COVID-19.
Cibiyar ta ce, “Kwayar cutar SARS-CoV-2 da bambance-bambancen ta suna yaduwa cikin sauƙi lokacin da mutane suka taru ko suka kusanci juna.
“Saboda haka, yayin da makarantu ke shirin sake budewa a cikin bullar annobar cutar COVID-19 a karo na hudu a Najeriya, NCDC ta yi kira da babbar murya ga makarantu da su yi taka tsantsan don hana karuwar yawan dalibai da ma’aikatan da suka kamu da cutar.
“Masu kula da makarantu su tabbatar da abubuwan da ke biyowa don rage haɗarin yaduwar COVID-19 a cikin makarantu; duban dumin jiki a kowacce rana a wuraren shiga. Wadanda ke da zafin jiki sama da 38 ° C kada a bar su shiga; a guji raba abubuwa kamar fensir, biros, abun goge rubu, ma’aikata, litattafai, da sauransu; dalibai da ma’aikatan da suka ji rashin lafiya su kasance a gida su nemi magani a cibiyar lafiya cikin gaggawa.
“Bugu da ƙari, NCDC ta ba da shawarar yin amfani da na’urorin gwajin gaggawa da aka amince da su a dakunan makarantun kwana na sakandare da harabar jami’o’i don gwada ɗalibai da ma’aikatan kan komawa makaranta da kuma waɗanda ke fuskantar alamun COVID-19 yayin zaman makaranta.”