By Abbas Yakubu Yaura
Sama da matasa 300 ne hukumar kula da samar da ayyukan yi ta kasa (NDE) ta horar dasu sana’o’in hannu a jihar Filato.
NDE a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce horon yana karkashin kungiyar (A-NOAS) da kuma (B-NOAS) da tsarin horarwar ciki gaggawa na ayyukan bayar da lamuni na sake tsugunar da su.
Wadanda suka kammala karatun za su karɓi fakitin da zasu ba su damar fara kasuwanci kuma su zama masu ɗaukar wasu aiki.
A wajen bude taron, ko-odinetan hukumar ta NDE na jiha, Ibrahim Abdulazeez, ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su kasance masu jajircewa, dogaro da kai da horar da sauran matasa.sannan ya ce rancen sake tsugunar da su da aka ba su abu ne wanda za’a mayar dashi, inda ya bukace su dasu tabbatar sun daidaita rancen a lokacin da aka kayyade domin sauran rukunin wadanda aka horar za su amfana.
Shugaban Sashen Haɓaka Ƙwararrun Sana’oi a hedkwatar NDE Abuja, Malam Yusuf Umar, ya gargaɗi waɗanda suka amfana da su yi amfani da tawali’u, gogewa da jajircewa don ba su damar samun nasara.
Wata wadda ta samu horon mai suna Tabitha Ibrahim ta yabawa NDE bisa wannan karimcin tare da yin alkawarin yin amfani da damar da gwamnatin tarayya ta basu.