By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar samar da aikin yi ta kasa (NDE) ta fara bayar da wani horo na kwanaki biyar ga matasa da mata 50 da basu da aikin yi a Kano a kan harkar aikin noma.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwar ranar Litinin a Kano, Ko-odinetan NDE na jihar, Malam Idris Sani Yakasai, ya ce makasudin gudanar da horon shi ne samar da ayyukan yi ga matasa.
Sannan ya kara da cewa hakan zai taimaka “Don inganta hanyoyin noma, kawar da shan barasa da ke da alaka da ayyukan noman gargajiya da kuma kara samar da abinci a jihar da kuma tarayya.”
Ko-odinetan ya ce horon yana kuma nufin rage yawan kaura zuwa wasu garuruwan da matasa ke yi.
Ya kara da cewa NDE na da niyyar ba su wasu rancen sayen injuna, wanda zai ba su damar shiga cikin karkara.
Yakasai ya ce wadanda aka horas din kuma za a dauki su a matsayin masu sana’o’in dogaro da kai domin za su iya karban wasu kudade ga manoman don ayyukan.
“Baya ga haka za su iya daukar wasu ma’aikata saboda yawancin shirye-shiryen NDE suna da tasiri da yawa idan aka horar da mutum kan fasaha zai iya horar da wasu mutane, ta yin hakan za a dauki matasa da yawa aiki a cikin al’umma”.
Saifullahi Sulaiman, daya daga cikin mahalarta taron, ya godewa gwamnatin tarayya bisa irin wannan horon, sannan ya yi alkawarin aiwatar da abin da suka koya a karshen kwas din.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara yawan wadanda za su halarci horon na gaba, ya kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi hakan, domin kara samar da ayyukan yi.
Shi ma Abdul-Rasheed Mohammed, wani mahalarci, ya yaba da wannan karimcin, yana mai cewa, “ horon ya dace da ni don dogaro da kai da kuma samar da aikin yi.”