Hukumar dake da alhakin dakile safarar miyagun kwayoyi, NDLEA ta bankado wasu jahohi guda uku dake rarraba miyagun kwayoyi wanda suka hada da koken da yakai nauyin kilograms 843 zuwa sauran jahohin kasar nan.
Jami’an NDLEA sunyi nasarar cafke ma’aikatan gidan sarrafa miyagun kwayoyi guda bakwai a wuri daban-daban cikin Jahohi uku wanda suka hada da Nasarawa, Benue da Kogi. Kamar yadda Jaridar Pm news ta wallafa a shafinta
Femi Babafemi mai magana da yawun jami’an NDLEA, ya bayyana hakane a wani jawabinsa a ranar Talata, yace a yunkurin jami’an na ganin an daina safarar miyagun kwayoyi ta kan tituna, jami’an sunyi arangama da Augustine Emmanuel, mai shekaru 45 yana kokarin shigar da kwayoyin ta hanyar ruwa daga Edo zuwa Kogi.
KARANTA:- Majalisar dokokin Jihar Kano ta gayyaci Muhyi Magaji-Rimingado da ya gurfana a gabanta
Yace anyi nasarar cafke su a ranar Litini 12 ga watan July 2021 a garin Jetty Idah, a Jahar Kogi, inda aka kama wata mota kirar Toyota Avalon number: Lagos SMK 345 CG dauke da lodin muggan kwayoyi masu nauyin kilograms 487 daga Agenebode Jahar Edo zuwa Jetty Idah Jahar Kogi.
An kwace su sannan anyi nasarar cafke shugaban su.
A wani labarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zauna da Yan majalisu 109 misalin karfe 8:00 a ranar Talata a Vila
An sanar da lokacin zaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Yan majalisun lokacin da Jagoran Yan majalisu Ahmad Lawan yake Jagorantar zaman Majalisa.
Ade 27 ga watan Aprilu 2021 ne, Yan majalisu suka yanke shawarar sanya lokacin tattaunawa da Muhammadu Buhari don duba yanayin rashin tsaro dake addabar kasar.
Kamar dai yadda sakon gayyatar zaman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da Yan majalisu ta kasan ce.
“Na rubuto wannan takardar don in sanar da Jagoran Yan majalisu cewar Muhammadu Buhari ya shirya zama tare da Yan majalisu tarayyan Najeriya ranar 13 ga watan July, 2021 da misalin karfe 8:00 na dare a ranar Talata.”
“Zamu zauna a babban dakin taro na Banquet, a cikin Vila Abuja.”