By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Edo, a ranar Alhamis, tace ta kama mutane 20 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.
Mista Buba Wakawa, Kwamandan hukumar na jihar ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Benin.Wakawa ya kara da cewa wadanda aka kama a watan Oktoba sun hada da maza 18 da mata biyu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito haramtattun kwayoyi da aka kama daga hannun wadanda ake zargin sun kai kilogiram 2,390,854 na tabar wiwi da ake zargin mutanen da ita, da kuma abubuwan da suka shafi kwakwalwa.
Ya kuma shaida wa manema labarai cewa, wasu gonaki da ake zargin tabar wiwi ce masu girman kadada 6.9 ne rundunar ta lalata a cikin wannan lokacin.
Kazalika Wakawa ya kuma kara da cewa, rundunar ta samu wasu laifuka guda 11 a cikin wannan lokuta, yayin da ake ci gaba da sauraron kararraki 32 a gaban kotu.
Ya kara da cewa rundunar ta kuma shawarci masu shaye-shayen miyagun kwayoyi 13 da suka hada da maza tara da mata hudu