Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama hodar ibilis wato koken mai nauyin kilogiram 9.30 wanda kudinta ya haura Naira biliyan 2.7 a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Mista Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce an kama wani matashi mai shekaru 32 da haihuwa mai safarar miyagun kwayoyi a kasar Laberiya, Maduabuchi Chinedu, tare da kayan.
Babafemi ya ce wanda ake zargin wanda ya fito daga kauyen Obaha Okigwe, a karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo, ya zauna ne a kasar Laberiya inda yake aikin hakar ma’adinai.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani bincike na hadin gwiwa na jirgin Ethiopian Airlines mai lamba 911 a filin jirgin Abuja a ranar 24 ga watan Nuwamba.
Ya ce hodar iblis mai nauyin kilogiram 9.30, an nade shi ne a cikin abun nade alawa aka boye a cikin jakunkunan wanda ake zargin. A yayin hirarsa ta farko, Chinedu ya yi ikirarin cewa ya bar Najeriya ne a shekarar 2018 inda ya zauna a kasar Laberiya wanda a yanzu yake da takardar izinin zama dan kasar.
“Duk da haka, ya kara da cewa yana cikin matsin tattalin arziki da bukatar samun kudi don yi wa mahaifiyarsa maganin matsalar ido ya sa ya nemi taimako daga abokinsa a Laberiya,” in ji sanarwar.
Chinedu ya ce abokin shi ne ya gabatar da shi da wani abokinsa da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wanda a karshe ya ba shi wannan koken ya kai Abuja kan kudi Naira miliyan daya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Babafemi ya ruwaito shugaban NDLEA, Bigediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya yabawa hafsoshi da jami’an hukumar ta NIA na hukumar bisa lura da aiki tare da sauran jami’an tsaro a filin jirgin.