Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gano kwayoyin Tramadol miliyan 13 a wani katafaren gida da ke unguwar Lekki a jihar Legas.
Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a safiyar ranar Litinin din nan.
Babafemi ya ce an kai sumame ne a ginin da ke unguwar Victoria Garden City (VGC) a Legas ranar Litinin.
KARANTA KUMA: NDLEA Ta Kama Dan Kasar brazil Dauke Da Hodar Iblis
“Wani kwalin maganin VGC! Kamar yadda katafaren gidan nan da ke cikin highbrow VGC Lekki Legas, hoton nan, ba mutane ne suke zama a ciki ba, amma ya kasance yana ajiye sama da kwayoyin Tramadol miliyan 13 na 225mg ta wani hamshakin attajiri yanzu yana hukumar NDLEA. Cikakkun bayanai zai zo nan gaba, ”ya wallafa a shafin Twitter.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Babafemi ya ce an damke mai kula da kwayoyin maganin kuma yanzu haka yana tsare.
A wani labarin kuma: Najeriya Za Ta Samu Zaman Lafiya Kafin Buhari Ya Bar Ofishi
Najeriya za ta kasance kasa mafi aminci da tsaro kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Wannan na zuwa ne a cewar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadin nan a wajen taron lacca karo na 20 na daliban da suka kammala kwas na 69 na kwalejin tsaro ta Kasa (NDA), da ke Kaduna.