Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta cafke Shugaban Kmfanin saida magunguna na Marvelrock Pharmaceuticals and Stores Limited, Orakwe Chibuike Celestine.
An kama Celestine ne a babban birnin Tarayya Abuja bisa zargin laifin yin cinikin haramtattun kwayoyi da sarrafa su a kafafen yanar gizo.
Wanda ya kammala karatu kan harkokin kasuwanci wato Business Administration a Jami’ar Abuja ya yi wa kamfanin nasa na harhada magunguna rajista a ranar 16 ga Disamban shekarar 2014.
An yi rajistar tare da takardar shaidar da goyon bayan wani mai lasisin magunguna, wanda ya fice daga cikin yarjejeniyar a cikin shekarar 2017.
Amma wanda ake zargin ya ci gaba da gudanar da sana’ar tare da shigar da ita a dandalin yanar gizo a shekarar 2019, kamar yadda kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba.
An fara sa ido kan Celestine a watan Oktoba 2021 lokacin da ya tallata kayayyaki irin su Tramadol, allurar Ketamine Hydrochloride, Allunan Hypnox flunitrazepam, da sauransu, a shafin yanar gizo.
Tsakanin 26 ga Oktoba 2021 zuwa 8 ga Agusta 2022, tawagar jami’an hana shan miyagun kwayoyi da lamarin ke hannunsu sun tabbatar da cewa yana sayar da Tramadol 225mg da sauran magunguna ta yanar gizo.
“An kama wanda ake zargin dauke da wasu nau’ikan Tramadol da Swiphnol, Rohypnol a ranar Litinin 8 ga watan Agusta a wata mashaya da ke unguwar Jabi a Abuja.”
Shugaban hukumar ta NDLEA Mohamed Buba Marwa ya ce bincike da aka gudanar wanda ya kai ga kama dan kasuwar ya kamata ya zama wani sako mai karfi ga masu amfani da yanar gizo wajen siyar da miyagun kwayoyi.