Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, reshen jihar Oyo, ta ce ta kama masu safarar miyagun kwayoyi 330 tare da hukunta guda 48 a jihar a shekarar 2021.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, Dr Wale Ige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Misis Mutiat Okuwobi, ta fitar ranar Lahadi a Ibadan.
Ige ya ce, wadanda ake zargin sun hada da maza 297 da mata 33, an kama su ne da laifin yin mu’amula da kwayoyi irin su Cannabis sativa, Tramadol, Diazepam, Rohypnol, Colorado, Codeine, Chocolate, codeine da sauran abubuwan da suka shafi maye.
Ige ya ce an gurfanar da wadanda ake zargi 101 a gaban kotu yayin da 48 daga cikinsu aka yanke musu hukunci kan laifuka daban-daban na miyagun kwayoyi tare da dauri daga watanni shida zuwa daurin rai da rai a cikin shekarar da ta gabata.
Ige Kuma Kara da cewa, rundunar ta samu nasarar kama kilogiram 3,543.96 na Cannabis sativa da sauran abubuwan da suka hada da narcotic da psychotropic a lokacin da take gudanar da aikin ta.