Jami’an hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wani tsohon dan wasan kwallon kafa, Okafor Emmanuel Junior a filin sauka da tashin jirgin saman Murtala Muhammed da ke dauke da hodar ibilis mai nauyin kilo 1.40 a boye a cikin jakunkunansa.
Channels TV ta ruwaito cewa, An kama matashin mai shekaru 33 a ranar Litinin bayan ya taso daga Sao Paulo na Brazil inda ya biyi ta Adis Ababa, a cikin wani jirgin saman kasar Habasha, bayan da jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi suka gano cewa ya boye haramtattun kayayyaki a cikin jakunkunansa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan tawayen Tigray Sun Janye Daga Yankin Amhara
A cewar hukumar, Okafor ya bayyana cewa, shi tsohon dan wasan kwallon kafa ne na Jami’ar Asibitin Koyarwa na kasa, UNTH wato Enugu FC, inda ya buga mata wasa har tsawon shekaru hudu kafin ya tafi kasar Sri Lanka a shekarar 2014.
Ya ci gaba da cewa ya koma Brazil ne daga Sri Lanka bayan ya buga wasa na kaka biyu amma bai iya ci gaba da buga kwallo a Brazil ba saboda rashin takardun izinin dsga hukumomi.
A halin da ake ciki kuma, wani Dan najeriya dake zaune a Brazil da ya dawo gida , Ibeh Chinedu Damian, shima ya shiga hannun hukumomi a ranar Litinin, bayan ya isa filin jirgin saman Legas daga Sao Paulo na Brazil ta jirgin saman kasar Habasha.
An gano Ibeh ya boye hodar ibilis mai nauyin kilogiram 3.20 wanda aka fi sani da ‘Lucci’ a cikin jakunkunan sa guda biyu.
A cikin bayaninsa, ya ce za a biya shi miliyan uku da dubu dari daya (N3,100,000) domin samun nasarar isar da kwayoyin a cikin kasa Najeriya.
Hakazalika, yunkurin da wata ‘yar kasuwa mai shekaru 32, Misis Pamela Odin ta yi na safarar kwayoyin Rohypnol mai nauyin kilogiram 2.150 ta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, NAIA, dake Abuja zuwa Istanbul, na kasa Turkiyya, ya ci tura, bayan jami’an hukumar ta NDLEA sun yi nasarar kamata.
An kama matar ne a ranar Juma’a yayin da take yunkurin shiga jirgin saman Turkiyya dauke da maganin a boye a cikin barkono da kuma wasu cikin kayan abinci.
Ta bayyana cewa tana da wani gidan cin abinci a birnin Istanbul na kasar Turkiyya ne, amma ta zo Najeriya ne domin ganin ‘yan uwanta da kuma siyan abinci domin kasuwancinta na sai da abinci.
A WANI LABARIN KUMA: Daliban Iran Sun Yi Arangama Da ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma A Tehran
Daliban kasar Iran sun yi arangama da jami’an tsaro a wata babbar jami’ar Tehran, a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula sakamakon mutuwar Mahsa Amini, kamar yadda kafafen yada labaran kasar da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka sanar.
Amini ‘yar Kurdawa ‘yar kasar Iran, mai shekaru 22, ta mutu ne a ranar 16 ga watan Satumba, kwanaki bayan da aka tsare ta bisa zargin karya ka’idojin tilasta mata sanya hijabi da tufafi masu kyau, wanda ya haifar da zanga-zanga mafi girma a Iran cikin kusan shekaru uku.