Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kwace wasu kadarori kusan 286 da asusun ajiya na banki 600.
Hukumar ta bayyana cewa baki daya wadannan kadarorin sun kasance na barayin kwayoyi ne, kuma an kama su tsakanin watan Janairu 2021 zuwa Agusta 2022.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, shine ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ya ce kadarorin sun hada da manyan motoci 249 da wasu gidaje 37.
Kamen da hukumar tayi ya zo ne a daidai lokacin da ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da muggan kwayoyi da laifuka ya ware Najeriya a matsayin wata kafa da bata gari kan yi amfani da ita wajen safarar muggan kwayoyi.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sake Duba Albashi Malaman Jami’o’i
A cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, tun shekara ta 2004 “masu safarar muggan kwayoyi ke kara yin amfani da kasashen yammacin Afirka, ciki har da Najeriya wajen safarar hodar ibilis daga Kudancin Amurka zuwa Turai da Arewacin Amurka.
Kasar na da yawan masu shan muggan kwayoyi saboda ci gaba da samar da magunguna da aka kera ba bisa ka’ida ba da kuma karkatar da su da ke dauke da magungunan sinadaran narcotic da abubuwan da suka shafi kwakwalwa.”
Da yake bayyana yadda hukumar ta kama wadannan kaya a cikin watanni 20 da suka gabata, Babafemi ya ce an kwace kadarori 286 tare da rike asusun banki 600.
Hukumar ta NDLEA ta kuma nuna cewa ta kama kudi Naira 871.53 wadanda kudin haramtattun kwayoyi tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Agusta 2022.
A wani labarin kuma: 2023: Ba Za A Hana ‘Yan Gudun Hijira Hakkinsu Na Kada Kuri’a Ba — INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta a ranar Talata ta ce kimanin ‘yan gudun hijira miliyan uku ne za su shiga zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Hukumar ta kara da cewa an samar da matakan tabbatar da duk ‘yan Najeriya da suka cancanta ciki har da ‘yan gudun hijira wajen ganin sun yi amfani da ikonsu a zaben badi.