Hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa wato NDLEA reshen Apapa dake jihar Legas ta ce ta ƙwace miyagun ƙwayoyi na kimanin naira biliyan shida tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana.
Kwamandan hukumar reshen Apapa, Ameh Inalegwu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa nauyin ƙwayoyin da suka ƙwace ya kai kilo dubu shatara da dari bakwai da uku da kuma dugo ashirin da biyar (19,703.25.)
Ya kuma bayyana cewa rundunarsa a shirye take domin ta shawo kan matsalar miyagun ƙwayoyi da ake shiga da su ƙasar ta teku.
Ya ce cikin miyagun ƙwayoyin da aka kama har da tramadol da hodar ibilis da wato codeine.
Wanann na zuwane a dai dai lokacin da ake bikin ranar yaki da shan miyagun kwayoyi ta duniya da majalissar dinkin duniya ta ware kowace ranar 26 ga watan yunin kowace shekarar.
A wani labarin kuma na daban.
Mutane 17 sun mutu a gidan Casun Afirka ta Kudu – ‘Yan sanda
Akalla matasa 17 ne aka tsinci gawarwakinsu a wani gidan rawa dake garin Birnin London na kudancin Afirka ta Kudu ranar Lahadi, in ji ‘yan sandan kasar
“Mun samu rahoto game da mutane 17 da suka mutu a wani wurin shakatawa na Scenery Park wanda ke gabashin London,” in ji wani babban jami’in ‘yan sanda na lardin, kammar yadda Birgediya Thembinkosi Kinana ya shaida wa kamfanin Dillancin Labaran faransaAFP.
Ya ce wadanda abin ya shafa na da shekaru tsakanin 18 zuwa 20.
Hotunan da ba a tantance ba da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin da ba a ga alamun raunuka ajikin su ba,, sun baje a kasa a filin kulob din.
Gidan talabijin na kasar ya nuna jami’an ‘yan sanda kasar na kokarin kwantar da hankulan gungun mutanen da suka taru a wajen kulab din da ke birnin, wanda ke gabar tekun Indiya, mai tazarar kusan kilomita 1,000 (mil 620) da kudancin Johannesburg.