Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa mutane hudu ne suka mutu yayin da aka ceto daya daga cikin baraguzan ginin da ya rufta a titin Oye Sonuga, Palm Avenue, a Mushin, Legas.
Daily Post ta ruwaito cewa, Ko’odinetan NEMA shiyyar Kudu Maso Yamma, Mista Ibrahim Farinloye ne ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a wata tattaunawa ta wayar tarho.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Yankewa Wani Dan Sanda Hukucin Daurin Rai-Da-Rai
Ya ce maza biyu da mata biyu sun mutu, yayin da aka ceto mutum daya a baraguzan ginin.
Tun da farko dai gwamnatin jihar Legas ta kuma ce za ta binciki musabbabin rugujewar ginin.
Kwamishinan tsare-tsare na jiki da raya birane, Mista Omotayo Bamgbose-Martins, yayin da ya ziyarci wurin ginin bene mai hawa uku, ya ba da umarnin a rusa ginin nan take saboda dalilai na tsaro da kuma dakile kara rugujewar wani sashi na ginin.
Ya kuma umurci hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) da dakin gwaje-gwajen kayayyaki na jihar Legas da su bankado musabbabin faduwar ginin.
.
A WANI LABARIN KUMA: Hukumar Kula Da Ayyukan Yan sanda Ta Yi Martani Kan Cin zarafin Teju Moses
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) a ranar Juma’a ta bayyana cin zarafin da aka kai wa Insfecta Teju Moses, ‘yar sandan da ke tare da Farfesa Zainab Abiola, a matsayin dabbanci da rashin mutunci.
Mista Ikechukwu Ani, shugaban sashin kula da kafafen yada labarai da hulda da jama’a na PSC, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce harin da aka kai Teju barazana ce ga tsaron kasa kai tsaye idan aka yi la’akari da yunkurin yin izgili ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da abin da hakan ya ke nufi.