Hukumar kula da wutar lantarki ta Nigeria NERC, ta amince kwamfanoni 11 da ke rarraba wutar lantarki a Nigeria (DisCos) su kara kudin kudin wutar lantarki da kaso 50.
Wannan na zuwa ne watanni biyu bayan da ta ƙara kudin wutar lantarkin da ya jawo cece kuce a watan Nuwamba 2020.
A cewar wata takardar doka biyan kudin wuta (MYTO) dauke da sa hannun sabon shugaban hukumar NERC, Engr. Sanusi Garba, a ranar 30 ga watan Disamba 2020, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Talata, sabon karin kudin wutar lantarkin zai fara aiki ne a ranar 1 ga watan Janairu 2021.
A sabuwar dokar mai lamba NERC/225/2020, hukumar ta ce ta yi la’akari da karin kudin shigar kasar da kaso 14.9% a watan Nuwamba 2020, da farashin Dala akan Naira N379.4/$1 a watan Disamba 2020, da kuma karfin samar da lantarkin na kaso 1.22% da kuma kudaden ajiya na CAPEX, ka fin ta kara kudin lantarkin a yanzu.
Wannan sabon karin kaso 50 na kudin wutar zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Yuni 2021 yayin da ake sa ran farashin CRT zai tashi daga watan Yuni zuwa Disamba 2021, inda ake sa ran nan ma kudin wutar lantarkin ya karu, a cewar hukumar NERC.
Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin watan Disamba 2021, hukumar NERC ta yi nuni da cewar tana kan sabunta kudin wutar lantarki, kuma biyan sabon kudin zai fara aiki ne daga watan Janairu 2021.
Hukumar NERC ta kara kudin da ta ke cajar kamfanonin DisCos a watan Satumba amma hakan ya jawo cece kuce daga kwastomomi da kuma ƙungiyoyin kwadago, inda ya tilasta gwamnati soke sabon farashin a wancan lokaci.