Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta kori kocin Nigeria Kuma Dan kasar Jamus Gernot Rohr, ba tare da bata lokaci ba, inda ta nada Mista Augustine Eguavoen, wanda a halin yanzu shi ne daraktan tsare-tsare na hukumar kwallon kafar kasar a matsayin kocin rikon kwarya.
Rohr ya shafe watanni 64 yana jan ragamar Mai rike da gambun gasar zakarun Afirka har sau uku, wanda ya sa ya zama koci mafi dadewa a Najeriya.
Bayan wani taro ta kafar Intanet da kwamitin gudanarwa na NFF a ranar Lahadi ya gudanar, an yanke shawarar cewa Eguavoen zai yi aiki tare da Salisu Yusuf; Paul Aigbogun (Mataimakin Koci); Joseph Yobo (Mataimakin Koci); Dr Terry Eguaoje (Mataimakin Koci) da Aloysius Agu (Mai horar da masu tsaron gida).
An nada tsohon kyaftin din Najeriya Augustine ‘Jay Jay’ Okocha, Nwankwo Kanu da Garba Lawal amatsin jakadu masu bada shawara ga mambobin Rikon kwaryar.
Babban Sakataren Hukumar NFF, Dr Mohammed Sanusi, ya ce: “Dangantaka tsakanin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya da Mista Rohr ta zo karshe. Mun gode masa da irin ayyukan da ya yi wa Super Eagles da Najeriya.
“Muna kuma so mu gode wa Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Tarayya saboda hadin kai da suke bayarwa.”
Eguavoen, wanda tsohon kyaftin din Najeriya ne, shi ne kocin tawagar a lokacin da ta kare a matsayi na uku a gasar cin kofin Afrika da aka yi a Masar a shekara ta 2006. Ya kasance kyaftin a filin wasa lokacin da Super Eagles ta dauki kofin Afirka a karon farko a waje, Wanda ya gudana a kasar Tunisiya shekaru 27 da suka gabata.
Yanzu zai jagoranci tawagar yayin da za ta fara shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 33 da za a yi a Kamaru daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun 2022, kuma har sai an nada wani babban koci.