An zabi Ibrahim Musa Gusau a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF.
An zabi Gusau ne a babban taron hukumar ta NFF na zabe karo na 78 wanda aka gudanar a Benin, jihar Edo.
Ya samu kuri’u 21 inda ya doke abokin takararsa na kusa da tsohon mataimakin shugaban kasar Ist Barista Seyi Akinwunmi wanda ya samu kuri’u 12, inji rahoton jaridar The Nation.
KARANTA KUMA: NFF TaKori Mai Horas Da Yan Wasan Super Eagles
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Duk da cewa Gusau bai samu kuri’u 22 da ake bukata ba don samun nasara kai tsaye a zaben farko, sauran ‘yan takarar sun fice daga zaben da za a sake yi.
Amaju Melvin Pinnick shi ne tsohon shugaban hukumar.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, ranar Alhamis ne kotun daukaka kara ta baiwa hukumar kwallon kafa ta Kasa NFF dakatar da hukunci gabanin taron babban zaben hukumar NFF.
A wani labarin kuma: ‘Yan Sanda Sun Binciko Mutuwar Wani Yaro Bayan Anyi Masa Allura
Rundunar ‘yan sanda a Legas ta fara gudanar da bincike kan mutuwar wani karamin yaro da ya mutu bayan da aka yi masa allura a wani asibiti da ke unguwar Ogombo a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN lamarin a ranar Alhamis din nan.