Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMe ta yi hasashen ambaliyar ruwa a wasu jihohi 34 a cikin kwanaki uku masu zuwa.
Hukumar ta ce, ruwan sama na iya zuwa da yawa, wanda zai iya haifar da ambaliyar ruwa a ranar Talata zuwa Laraba da kuma Alhamis.
Kazalika hukumar ta bayyana jihohin da abin zai shafa da suka hada da Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Yobe, Kebbi, Niger, Babban birnin tarayya Abuja, Fulato Adamawa, Taraba, Kwara, Oyo, Legas, Ondo, Ogun, Edo, Delta, Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom, Benue, Enugu, Ebonyi, Imo, Anambra, Abia da kuma Jihar Kogi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An tumbuke Kakakin majalissar Jihar Kebbi
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar Muntari Yusuf Ibrahim ya fitar a yau Talata.
Hukumar ta kuma bayyana cewar, mafi karancin ambaliyar ruwan za’asame shi ne a kan hanyoyi, matsugunai, da kuma gonakin, kana gadoji ka iya ruftawa, sakamakon haka, akwai yuwuwar motoci su rufta, da kuma samu karuwar hadarin mota.
Ta kuma gargadi jama’a da su kula matuka, domin kauce wa hadarin da ke tattare da ambaliyar ruwan saman. Bisa hasashen da hukumar ta yi.
A wani labarin Kuma na daban.
NDA ta tabbatar da kashe mata Manyan jami’ai 2, tare da Garkuwa da guda
Makarantar horas da Jami’an soji ta kasa ta tabbatar da kashe manyan jami’an ta biyu, Laftanar Cdr Wulah, da Flt Lt Cm Okoronwo, tare da garkuwa da Manjo Datong, a wani hari da yan bindiga suka kai makarantar a safiyar yau Talata.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar Manjo Bashir Muhd Jajira fitar a yau, ya ce, lamarin ya faru ne a cikin Afaka dake makaranta, da sanyin safiyar yau Talata.
Ya kara da cewa, Jami’an makarantar, tare da hadin gwuiwar jami’an Barikin 1 Division, da na rundunar horas da Jami’an sojin sama, da kuma sauran hukumomin tsaro, na kokarin farmakan yan bindigan.
Sanarwar ta ce “A safiyar yau wasu Yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, sun afka cikin makarantar horaswan na Afaka, inda suka kashe manyan jami’ai soji biyu, da kuma yin garkuwa da guda”
Kazalika sanarwar ta ce, ” Yankin Makarantar da kuma sabbin jami’an dake samun horo a Makarantar na cikin koshin lafiya. Inda kuma muke sanarwa da al’uma cewa, nan bada jima wa ba, za’a kama wadannan yan bindigan, sannan kuma za’a kubutar da jami’in da suka sace” inji sanarwar