• Hukumar kual shige da fice ta kasa, ta kubutar da Mata 4 daga hannun masu saffarar Mutane a jihar Jigawa.
• Mutanan na kan hanyar su ne ta zuwa birnin Tripoli na kasar Libya.
• Shugaban hukumar shiyar jiyar ne ya bayyana wa manema labarai wannan nasarar, inda ya hukumar ta kama wasu mutane da take zargi wurin safarar mutane.
Hukumar kula da shige da fice ta kasa ta ce, ta ceto mata hudu a hannun masu saffarar mutane a jihar Jigawa.
Kwanturolan hukumar shiyar jihar Mr Isma’il Abba ne ya bayyana wa manema Labarai hakan a garin Dutse babban birnin jihar Jigawa. inda ya ce, an ceto wadanda lamarin ya shafa ne a ranar Alhamis, a kyauyen Gurai dake karamar hukumar Babura na jihar.
Abba ya ce, jami’an hukumar ne su kayi nasarar kubutar da mutanan, a lokacin da suke bakin aiki a iyakar Kazaure-Babura zuwa kazaure.
Ya kara da cewa, wadanda aka kubutar suna da shekaru 16 zuwa 33, da a kayi kokarin saffarar su zuwa Tripoli babban birnin Libya, daga ikokin jihar Jigawa da Katsina.
Kazalika ya ce, Hukumar ta kama wasu mutane dake da halaka da masu saffarar mutane, inda ya ce, yanzu haka ana gudanar da bincike, Kuma mutanan da ake zargi sun fito ne daga jihohin Akwa Ibom, Lagos, Ogun da kuma jihar Osun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin Mota ya yi sanadiyar mutuwar Mutum 10 a Kwara
Shugaban hukumar ya ce, da yuwuwar a mika wadanda ake zargi ga hukumar yaki da saffarar mutane ta kasa wato NAPTIP.
Comments 1